Home Labaru Farmaki: Mayakan Boko Haram Sun Kai Wa Sojoji Farmaki A Jihar Borno

Farmaki: Mayakan Boko Haram Sun Kai Wa Sojoji Farmaki A Jihar Borno

797
0

A wani harin samame da mayakan Boko Haram suka kai a kan wani sansanin sojoji a Jihar Barno, sun kashe jami’an soji biyar tare da ji ma wasu da dama rauni.

Ana dai fargabar akalla an kashe sojoji biyar tare da wasu da dama da aka ce an ji ma rauni a lokacin da maharan suka kai samamen.

An kai farmakin a wani sansanin sojoji da ke Mararrabar Kimba, kimanin kilomita 130 zuwa Maiduguri.

Sojojin Bataliya ta 254 ne wadanda ke karkashin Birgade na Sojojin Musamman na 25 ke kula da wurin, kuma dukkan su zarata ne da ke karkashin rundunar ‘Operation Lafiya Dole.’