Home Labaru Korafin Zabe: Jam’iyyar PDP Ta Zargi INEC Da Sauya Bayanan Sakamakon Zabe

Korafin Zabe: Jam’iyyar PDP Ta Zargi INEC Da Sauya Bayanan Sakamakon Zabe

394
0
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

Jam’iyyar PDP ta zargi hukumar zabe da sauya bayanan sakamakon zaben shugaban kasa na shekara ta 2019 da ke kan na’urorin ta.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce a kokarin ta na sauya sakamakon zaben shugaban kasa na gaskiya, hukumar zaben ta fara sauya bayanan da ke kan na’urori masu kwakwalwa bayan ta riga ta aika sakamakon gaskiya tun a farko.

Ologbondiyan ya kara da cewa, hukumar zaben ta dauko hayar wasu kwararru a bangaren goge bayanai daga kan na’ura mai kwakwalwa domin su yi mata aikin sauya sakamakon zaben.

Jam’iyyar PDP, ta kara zargin hukkumar zabe da daukar wasu kwararrun da za su sauya rijistar masu zabe domin kara boye irin magudin da aka tafka a zaben shugaban kasa.

A karshe Ologbondiyan ya ce, za sudauko kwararru a bangaren gudanar da gwaji ta hanyar amfani da kimiyyar zamani domin su duba kayayyakin da aka yi aikin zaben shugaban kasa da su.

Leave a Reply