Home Labaru Farfesa Attahiru Jega Ya Tsunduma Fagen Siyasar Nijeriya

Farfesa Attahiru Jega Ya Tsunduma Fagen Siyasar Nijeriya

480
0
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa

Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, ya shiga fagen siyasar Nijeriya domin a dama da shi, inda tuni ya yanke shawarar shiga jam’iyyar PRP kamar yadda shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya bayyana.

Farfesa Attahiru Jega dai ya shugabanci hukumar zabe ta kasa tsakanin shekara ta 2010 zuwa 2015.

Bayan bakin jinin da ya yi a arewacin Nijeriya a shekara ta 2011, sakamakon bayyana Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya yi nasara, Jega ya samu farin jini a shekara ta 2015 bayan ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara.

Har yanzu dai ba a san takamaiman lokacin da Jega ya shiga jam’iyyar PRP ba, amma Balarabe Musa ya ce an fara tattaunawa da shi watanni uku da su ka gabata.