Home Labaru EFCC Ta Kai Farmaki Gidan Abdul-Aziz Yari

EFCC Ta Kai Farmaki Gidan Abdul-Aziz Yari

708
0
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, sun kai samame a gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul-Aziz Yari da ke garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.

Wata majiya ta ce jami’an hukumar da yawan su ya kai ashirin, sun dira gidan ne da misalin karfe 6 na yammcin ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka kai har zuwa karfe 11 na dare su na gudanar da bincike.

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko jami’an sun bankado wasu abubuwa a gidan, amma majiyoyi sun tabbatar da cewa, daga tsohon gwamnan har iyalan sa babu wanda ke cikin gidan a lokacin da jami’an su ka isa.

Haka kuma, an jiyo mazauna garin Talatar Mafara da su ka yi cincirindo a kofar gidan su na kabarbarin ‘Allahu Akbar,’ da nufin nuna adawar su da abin da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan.

A makon da ya gabata ne, dan takarar gwamnan jihar Zamfara na jam’iyyar APGA Sani Shinkafi, ya nemi wata kotu ta tilasta wa EFCC gudanar da bincike a kan mulkin Abdul-Aziz Yari.