Home Labaru Atiku Ya Dora Kangin Talauci A Kan Gwamnatin APC

Atiku Ya Dora Kangin Talauci A Kan Gwamnatin APC

216
0
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’yyar PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’yyar PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’yyar PDP Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta riga ta gama kassara al’amurran Nijeriya ta fuskar tattalin arziki.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Paul Ibe ya fitar, Atiku ya ce a tsawon shekaru hudu da su ka gabata, ‘yan Nijeriya sun yi rayuwa a cikin kangin matsanancin talauci.

Ya ce majalisar dinkin Duniya ta ankarar da ‘yan Nijeriya game da yadda gwamnatin APC ta kasa inganta tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan ya jefa sama da mutane miliyan 98 a cikin matsanancin talauci ta kowace siga.

Atiku Abubakar, ya kuma bayyana mamakin yadda gwamnatin APC da ‘yan kazagin ta su ka kasa cewa komai a kan kididdigar alkalumman talauci da majalisar dinkin Duniya ta fitar game da Nijeriya.