Wani tsohon sojin Najeriya da ya halarci yakin duniya na biyu Adamo Aduku, ya bukaci gwamnatin tarayya ta taimaka ta biya shi hakkokin sa na Fansho.
Aduku, wanda yanzu haka ke da shekaru 104 a duniya, na daga cikin tsaffin jami’an Sojin da babban Hafson Sojin Najeriyar ya karrama yayin wani biki a ranar tunawa da ‘yan mazan jiya da ya gudana a Lagos.
Da ya ke Magana da manema labarai, Adamo ya ce tun bayan da aka sallameshi daga bakin aiki cikin shekarar 1957 har yanzu bai samu hakkokinsa na barin aiki ba.
Cikin jawaban Aduku gaban Manema labarai, ya ce tun cikin shekarar 1942 ya shiga tawagar dakarun yammacin Afrika da aka yi amfani da su a yakin duniya na 2, inda kai tsaye aka zuba su a jiragen ruwa zuwa India suka gwabza yaki a Calcutta.
A cewar Tsohon sojin na Najeriya bayan dawowarsu gida a shekarar 1946 sun shiga tawagar horarwa a Lagos kafin daga bisani a sallame su a cikin shekarar.
ya kara da cewa a cikin shekarar 1950 ya sake komawa aikin soja kafin a sake sallamarsa a 1957, matakin da ya tilasta masa komawa fagen noma a kasarsa ta haihuwa wato karamar hukumar Ibejukolo Omala ta jihar Kogi.