Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Najeriya reshen jihar Nasarawa, Mahammad Huseni ya ce duk gwamnan da yaki amincewa da shirin gwamnatin tarayya na gina wa makiyaya Ruga a jihohinsu na neman a ci gaba da rikici ne.
Shugaban kungiyar Huseini, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da manema labarai a Lafia babbar birnin jihar Nasarawa, inda yake jaddada cewa shirin Ruga a jihohi 36 zai tabbatar da karshen rikici dake tsakanin manoma da makiyaya.
Ya bukaci gwamnoni masu shakka, su bi sahun takwarorinsu wajen shiga cikin shirin domin tabbatar da kawo karshen rikici dake aukuwa a jihohin su.
Ya ce a shirye Fulanin jihar Nasarawa suke, su bada goyon baya ga shirin gwamnatin tarayya akan kaddamar da shirin, inda ya roki sauran kabilu masu tunanin ana iya samun mummunar sakamako idan Ruga ta canja ra’ayi nan gaba.
A halin da ake ciki gwamnatin tarayya ta jingine shirin samar da rugar makiyaya sakamakon cece-kuce da aka rika yi kan batun.