Home Coronavirus Kano: An Dage Dokar Hana Fita Saboda Ramadan

Kano: An Dage Dokar Hana Fita Saboda Ramadan

597
0
San sassauta dokar kulle a Kano don jama'a su yi cefanen azumin watan Ramadan
Yadda kasuwar Sabon Gari mai cike da cinkoson jama'a ta kasance wayam a lokacin dokar hana fita

An sassauta dokar hana fita a jihar Kano domin ba wa jama’a damar yin cefane kafin fara azumin watan Ramadan.

A ranar Jama’a 25 ga watan Afrilun da muke ciki ne ake sa ran fara azumin Ramadan.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya dage dokar hana fita ta sa’a 24, daga karfe 6 na safe zuwa 12 na daren 24 ga Afrilu, 2020, a cewar mai magana da yawunsa, Salihu Tanko Yakasai.

Sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter ta kara da cewa daga nan kuma za a sake dawo da dokar hana fita na sa’a 24 har na tsawon mako guda.