Home Labaru Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Dalilin Kin Amincewa Da Buƙatar Erdogan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Dalilin Kin Amincewa Da Buƙatar Erdogan

179
0

Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske kan dalilan da suka sa gwamnati ta ƙi amincewa da bukatar shugaban Turkiyya Racib Tayyeb Erdogan na ba shi hadin kai wajen daukar mataki kan magoya bayan Fathullah Gullen da ƙadarorinsa da ke Najeriya.


Shugaba Erdoğan na Turkiyya ya ce wadanda suka shirya yi
masa juyin mulki a 2016 suna nan har yanzu a Najeriya suna
gudanar da harkokinsu inda ya nemi hadin kan Najeriya wajen
murkushe su.


Erdogan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar kwana biyu a
Najeriya, inda suka tattauna kan batutuwa tsakaninsa da
Shugaba Buhari.


Ba wannan ne karo na farko da Turkiyya take neman wannan
buƙatar ba, inda ko a baya ta sha neman hakan ta hannun
jakadanta da ke Najeriya, amma gwamnati taki.


Mai Magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu
yace matsayin shugaban kasar na ƙin rufe makarantu da asibitoci
da sauran harkoki na wadanda kasar ke zargi da yunkurin kifar
da gwamnati bai sauya ba.


Gwamnatin Erdogan na zargin mabiya fitaccen malamin addinin
Musuluncin nan da ke zaune a Amurka Fethullah Gulen da
yunkurin kifar da gwamnatinsa.

Wannan dai na da makarantu da asibitocin a Najeriya.