Home Labarai Yanzu Hanyar Abuja-Kaduna Babu Mahara Babu Fargaba – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Yanzu Hanyar Abuja-Kaduna Babu Mahara Babu Fargaba – Kwamishinan ‘Yan Sanda

23
0

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Yekini Ayoku, ya ce a
yanzu hanyar Abuja zuwa Kaduna ta samu lafiya ta yadda
matafiya za su bi ta ba tare da fargabar komai ba.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin
rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna Kaduna Mohammed Jalige
ya fitar, inda Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci matafiya su
kwantar da hankulan su domin hanya ta yi kyau.

Babban hanyar Abuja dai Kaduna ta zama shiga da Alwalar ka
saboda hare-haren ‘yan bindiga da ya tsananta.

Mohammed Jalige ya yi kira ga mutane cewa, rundunar ‘yan
sanda ta bukaci mutane su rika taimaka wa jami’an tsaro da
bayanan sirri domin taimaka wa wajen gano bata-gari a cikin
al’umma.