Dakataccen gwamnan babban bankin Godwin Emefiele,
ya roƙi babbar Kotun tarayya da ke zama a Legas ta bada
belin sa gabanin fara sauraren tuhumar da ake yi masa.
Wata majiya ta ce, Emefiele ya buƙaci Kotun ta taimaka ta bada umarnin a sake shi a matsayin beli, gabanin yanke hukunci a ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan sa.
Godwin Emefiele ya gabatar da buƙatar a gaban Kotu ne ta hannun lauyoyin sa a ƙaraƙashin babban lauya Joseph Daudu.
Har yanzu dai babu tabbacin ranar da za a gurfanar da Godwin Emefiele a gaban Kotun a kan tuhume-tuhume biyu masu alaka da mallakar bindiga da alburusai ta haramtacciyar hanya.