‘Yan majalisar wakilai sun watsa wa ‘yan Nijeriya ƙasa a
ido, dangane da kiraye-kirayen da ake yi na a dakatar da
ƙarin farashin man fetur.
Rahotanni sun ce, ‘yan majalisar sun yi watsi da kirayen- kirayen a dakatar da ƙarin farashin kuɗin man fetur daga Naira 537 zuwa Naira 617 kan kowace lita ɗaya.
Wannan dai ya na zuwa ne, akalla kwanaki shida bayan ‘yan majalisun sun amince a ba su tallafin Naira biliyan 70 daga cikin tallafin Naira biliyan 500 da aka shirya domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Sai dai ‘yan majalisar sun amince su kafa kwamitin wucin-gadi, wanda zai ƙunshi kowane yanki daga cikin yankuna shida da ake da su a Nijeriya.