Home Labaru Ana Gudanar Da Zaben Gwamnan Jihar Anambra

Ana Gudanar Da Zaben Gwamnan Jihar Anambra

56
0

Ana ci-gaba da gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra, zaben da ake ganin zai iya zama zakaran-gwajin-dafi kafin zaben shugaban kasa da za a yi a watanni 18 masu zuwa.

Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya, ta ce ta tura jami’an ta akalla dubu 35 domin kare lafiyar masu kada kuri’u da malaman zabe, sakamakon tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da ‘yan awaren Biafra.

Kungiyar IPOB dai ta janye haramcin da ta yi wa jama’a na fita zaben, a cikin sanarwar da ta fitar ta hannun kakakin ta Emma Powerful, inda ta yi gargadi a kan duk wani yunkuri na tafka magudi.

Sama da ‘yan takara 10 ne ke neman kujerar gwamnan jihar Anambra, amma masu sa ido su na kallon dan takarar jam’iyyar APGA Chukwuma Soludo da Andy Uba na Jam’iyyar APC da na Jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo a matsayin wadanda ke sahun gaba waje lashe zaben.

Rahotanni sun ce mutane sun fito a wasu yankuna, yayin da ake dari-dari a wasu yankunan saboda fargabar tsaro.