Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai, ya
nesanta kan sa daga kalaman aka ce ya furta cewa Shugaba
Tinubu ya yi amfani da addini wajen cin zaɓe.
El-Rufai ya ce ƙarya ce kawai tsagwaron ta, wadda aka ƙirƙiro ake jifar sa da ita.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da wani littafi yayin bikin ritayar Farfesa Ishaq Akintola na jami’ar jihar Legas, El- Rufa’i ya ce ya ƙi maida martani a kan sauya ma shi kalamai da aka yi ne saboda waɗanda su ka yi hakan ba su son gaskiya.
Ya ce kalaman da ya yi ana dab da rantsar da sabuwar gwamnati a kan siyasa da mulki a jihar Kaduna da batun tikitin Tinubu da Shettima kamata ya yi a ce an fahimce su da idon basira.
El-Rufa’I, ya kuma gode wa ƙungiyar MURIC da sauran waɗanda su ka riƙa kare shi ta hanyar bayyana haƙiƙanin saƙon da ya ke nufi a cikin kalaman da ya yi a wancan lokacin.