Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya shugaba
Bola Tinubu murnar zaɓen sa da aka yi a matsayin shugaban
kungiyar bunƙasa arzikn Afirka ta Yamma ECOWAS.
Kakakin tsohon shugaban kasa Malam Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Garba Shehu, ya ce al’ummar Afirka ta Yamma sun damƙa wa sabon shugaban Nijeriya gagarumin aiki, don haka akwai bukatar a taimaka ma shi don ganin bai bada kunya ba.
Buhari ya kara da cewa, ya na fatan Allah ya sa a farfaɗo da ECOWAS a matsayin ƙungiyar tabbatar da dimokraɗiyya, da kyakkyawan shugabanci da yaki da ta’addanci da sauyin yanayi a zamanin mulkin Tinubu.