Home Labaru El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni

El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni

381
0
El-Rufai Ya Bada Umurni Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni
El-Rufai Ya Bada Umurni Rufe Shagunan Saida Gas A Cikin Unguwanni

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bada umurnin rufe duk tashoshin saida iskar gas da ke wuraren zaman jama’a a fadin jihar.

El-Rufa’i, ya kuma roki mazauna jihar su kai rahoton wurarren da ake saida Gas a cikin jama’a ba tare da bata lokaci ba domin daukar matakin gaugawa.

Gwamnan, ya ce tashar gas na da hatsari sosai, wanda ya kamata a rika gudanar da harkar ne a wuraren kasuwanci, inda za a iya daukar matakan kariya.

El-Rufa’i, ya kuma kai ziyarar jaje ga iyalan Farfesa Simon Mallam, wanda ya rasa ran sa biyo bayan fashewar tukunyar Gas a unguwar Sabon Tasha da ke garin Kaduna, sannan ya ziyarci mutanen da lamarin ya shafa a babban asibitin St Gerald da ke Kaduna.