Home Labaru Dubban ‘Yan Jam’Iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Cross...

Dubban ‘Yan Jam’Iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Cross Rivers

12
0

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Cross Rivers Venatius Ikem, ya karbi sama da mutane dubu 5 da su ka sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Wata majiya ta ce, jam’iyyar PDP ta shirya taron karɓar dubban masu sauya shekar ne a kwalejin fasaha da ke Ogoja.

Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban jam’iyyar PDP ya ce dawowar tsofaffin ‘yan jam’iyyar da kuma sauya shekar wasu alama ce ta nasarar da jam’iyyar ke fatan samu a zaɓe mai zuwa.

Tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da su ka sake komawa da sabbin da su ka shigo sun fito ne daga kananan hukumomi biyar da ke jihar Cross Rivers.

Daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasan da su ka koma PDP akwai tsohon mashawarci na musamman ga tsohon gwamnan jihar Dakta Peter Oti.

Shugaban jam’iyyar PDP, ya kuma yaba wa dubban mutanen da su ka nuna mubayi’ar su ga sanata Agom mai wakilar jihar Cross Rivers ta arewa.