Home Labaru Kasuwanci EFCC Ta Fara Kama Masu Karbar Dala Daga Bankuna Da Bizar Bogi...

EFCC Ta Fara Kama Masu Karbar Dala Daga Bankuna Da Bizar Bogi – Bawa

134
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce ta fara kamen ‘yan Nijeriyar da ke karbar kudadden kasashen waje a bankuna da sunan fita kasashen ketare kasuwanci da neman lafiya ko karatu da sauran su da bizar bogi.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, akwai mutane da dama da ke neman kudin kasashen waje a bankuna da bizar karya, alhali su na amfani da kudadden ne a kasuwannin canji na bayan fage da wata manufa ta daban.

Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka, yayin da ke jawabi a cikin shirin ‘Siyasa A Yau’ na gidan talabijan na Channels.

Abdurrasheed Bawa, ya yaba da shirin babban CBN na sa ido tare da kama masu neman dala da manufar komawa kasuwannin canji na bayan fage don su ci kazamar riba, sakamakon yadda gwamnati ta janye ba ‘yan canji dala kai tsaye kamar yadda ta saba yi a baya.

A makonnin baya-bayan nan ne, babban bankin Nijeriya ya sanar da cewa zai hada gwiwa da hukumar EFCC wajen kama masu karbo dala daga bankunan da bizar bogi domin sayarwa a kasuwannin canji na bayan fage.

Leave a Reply