Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta sake kakaba wasu sabbin takunkumai ga gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar.
A baya dai, ECOWAS ta ba sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwanaki bakwai su maida hambararren Shugaban Kasar Mohammed Bazoum a kan karagar mulkinsa, ko kuma ta mamaye kasar.
Sai dai sojojin sun yi kunnen uwar shegu da matakin na ECOWAS, tare da cewa za su tsaya kai da fata wajen ganin sun kare kasarsu daga duk wata barazana.
Haka kuma, Nijar ta sanar da yanke duk wata alaka tsakaninta da kasashen Nijeriya da Togo da Amurka da kuma Faransa, lamarin da yasa ta rufe sararin samaniyarta.
Bayan cikar wa’adin na ECOWAS, kungiyar ta kira wani taron gaggawa da za a gudanar ranar Alhamis, domin duba halin da ake ciki a Nijar da kuma sanin matakan da za a dauka a nan gaba.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja, Kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale, ya ce an kakaba takunkuman ne a kan daidaikun mutane da kungiyoyin da suke duk wata hulda da gwamnatin sojan Nijar, kuma ya ce an aiwatar da takunkumin ne ta hannun bankin CBN.