Home Labaru Hukumar ICPC Ta Waiwayo Kan Minista Kuma Surukin Tsohon Shugaba Buhari

Hukumar ICPC Ta Waiwayo Kan Minista Kuma Surukin Tsohon Shugaba Buhari

144
0

Hukumar yaki da rashawa da nau’ukan zamba ICPC, ta fara
bincike a kan tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami.

Rahotanni sun ce, hukumar ta na bincike ne game da zargin cin amanar ofishin sa da ya yi lokacin da ya kasance Ministan shari’a.

Tun daga karshen shekara ta 2015 har zuwa watan Mayu na shekara ta 2023, Abubakar Malami shi ne Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan wata kungiya mai suna HEDA ta rika aike wa hukumar ICPC korafin cewa tsohon Ministan shari’ar ya tafka rashin gaskiya.

Leave a Reply