
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta ce ta kama ƙwayar Tramadol akalla miliyan biyu da maganin tari na Codeine a filin jirgin sama na Muratala Muhammad da ke Legas.
A Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an shigo da ƙwayoyin ne daga kasashen Pakistan da Birtaniya.
NDLEA ta ƙara da cewa, an ƙwace kayan a ranar 10 ga watan Maris, inda aka samu ƙwaya samfurin Co-codamol dubu 349 da 800, wadda gwamnati ta haramta.
Sai kuma a ranar 15 ga watan Maris, jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar na hukumar Kwastam sun kama ƙwayar Tramadol miliyan 1 da dubu 584 a filin jirgin.
Sanarwar, ta ce waɗanda su ka yi safarar ƙwayoyin sun yi amfani da motar jigilar kaya ta cikin filin jirgin ne.













































