Home Home Martani: PDP Fatan Tarwatsewar Nijeriya Ta Ke Yi – Adesina

Martani: PDP Fatan Tarwatsewar Nijeriya Ta Ke Yi – Adesina

77
0
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi zargin cewa, jam’iyyar PDP ta na fatan Nijeriya ta yamutse in dai yin hakan zai iya sa mulki ya koma hannun ta.

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi zargin cewa, jam’iyyar PDP ta na fatan Nijeriya ta yamutse in dai yin hakan zai iya sa mulki ya koma hannun ta.

Kakakin Shugaban Ƙasa Femi Adesina ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Femi Adesina ya bayyana haka ne, biyo bayan wata sanarwa da Hukumar tsaro ta SSS ta fitar cewa wasu ɓatagari na shirya yadda za a yi tashe-tashen hankula a Tsakiyar Nijeriya saboda matsalar wutar lantarki.

Duk da dai hukumar tsaron ba ta ambaci suna ba, amma jam’iyyar PDP ta ce ta na tsoron kada matsalar wutar lantarkin  ta haifar tarzomar da ta fi ta #EndSARS muni a Nijeriya.

Da ya ke maida martani, Adesina ya ce maimakon PDP ta yi wa Nijeriya fatan mummunar tarzoma, kamata ya yi ta yi aikin da zai kawo haɗin kai da zaman lafiya a Nijeriya.