Home Labaru Mun Kama Wadan Da Muke Zargi Da Hannu A Fasa Gidan Yarin...

Mun Kama Wadan Da Muke Zargi Da Hannu A Fasa Gidan Yarin Oyo – Makinde

9
0

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya ce wasu manyan ‘yan tada zaune tsaye sun shiga hannu bisa zargin su da hannu a fasa gidan yarin jihar.

Da ya ke jawabi yayin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, gwamnan ya ce har yanzun ana ci-gaba da bincike a kan lamarin.

Sai dai gwamnan bai bayyana sunayen waɗanda ake zargin ba, sannan bai fayyace ko su na daga cikin fursunonin da su ka tsere ba.

Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa, daga cikin su akwai wani sanannen dan ta’adda mai suna Sunday Shodipe, da wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Iskilu Wakili.