Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce ta kama jami’an banki a cikin bata-garin da su ka kware wajen saida sabbin takardun kudin da aka sauya wa fasali.
Da ya ke bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kakakin hukumar DSS Peter Afunanya, ya ce wasu bata-gari daga cikin kungiyoyi su na da hannu wajen saida sabbin kudaden da aka sauya wa fasali.
Ya ce a cikin ayyukan hukumar DSS, sun tabbatar da cewa wasu ma’aikatan bankunan kasuwanci su na taimaka wa bata-gari wajen jefa ‘yan kasa cikin mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki.
Duk da cewa Afunanya bai ambaci sunan wani banki ko kuma a jihar da lamarin ya faru ba, hukumar DSS ta gargadi masu saida kudin su daina aikata wannan aiki na jahilci.
You must log in to post a comment.