Home Home Ku Yi Amfani Da Kwanaki 10 Wajen Mayar Da Tsofaffin Kudin Ku...

Ku Yi Amfani Da Kwanaki 10 Wajen Mayar Da Tsofaffin Kudin Ku Banki – Sanusi

35
0

Khalifan Tijaniyya Sanusi Lamido Sanusi II, ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya su yi amfani da karin wa’adin da bankin CBN ya yi domin kai tsofaffin kudaden su bakunan da su ke ajiya.

Ya ce daga yanzu zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu, duk mai tsofaffin takardun kudaden ya je ya ajiye su a banki, ya na mai nuni da cewa, ajiye kudaden a bankuna zai taimaka wajen yin mu’amala da kudade a Nijeriya.

Khalifa Sanusi Lamido, ya ce bankin CBN ya bada tabbacin cewa, zai sa ido a kan bankuna domin tabbatar da ganin an musanya wa kowa tsofaffin kudaden da sabbi.

Haka kuma, Khalifan ya bukaci ‘yan Nijeriya su taimaka wajen sa ido a kan wadanda ke yin cuwa-cuwa a bankuna.

Ya ce akwai mutanen da ke karbar kudade daga wajen wasu ‘yan siyasa ko masu laifin da ba za su iya zuwa bankuna da sunan su ba.