Home Labaru Dole PDP Ta Mika Shugabancin Kasa Ga Yankin Kudu Maso Gabas –...

Dole PDP Ta Mika Shugabancin Kasa Ga Yankin Kudu Maso Gabas – Ikpeazu

14
0

Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu, ya ce ya na da muhimmanci jam’iyyar PDP ta mika tikitin takarar shugaban kasa na shekara ta 2023 zuwa yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Okezie Ikpeazu ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Abia, inda ya ce yankin kudu maso gabas bai taba samar da shugaban kasa ba a Nijeriya.

Ya ce ya kamata a mika wa yankin tikitin takarar shugaban kasa na shekara ta 2023 ba tare da bata lokaci ba, domin an dade ana maida yankin tamkar saniyar ware.

Gwamnan Ikpeazu, ya ce kamar yadda PDP ta karkatar da shugabancin ta zuwa yankin arewa, ya kamata kujerar shugaban kasa ta koma yankin kudu maso gabas.