Home Labaru Dalilin Da Ya Sa Jami’An Mu Su Ka Kama Shugaban KASUPDA –...

Dalilin Da Ya Sa Jami’An Mu Su Ka Kama Shugaban KASUPDA – EFCC

19
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce jami’an ta sun kama shugaban Hukumar Raya Birane ta Jihar Kaduna KASUPDA, Isma’il Umaru Dikko a kan wasu al’amurra na hukumar.

Rahotanni sun ce, jami’an hukumar EFCC sun mamaye helkwatar KASUPDA a ranar Litinin da ta gabata, tare da dauke Isma’il Dikko a cikin wata bakar mota kirar Hilux Toyota zuwa ofishin su na Kaduna.

KASUPDA dai ita ce hukumar da ke kula da ci-gaba da tsare-tsaren gine-gine a biranen jihar Kaduna, wadda ta yi suna wajen rusa gine-gine a Kaduna.

Mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ya ce ba wai an gayyaci Dikko a kan zamba ne ba, illa saboda wasu lamurra da su ka shafi ka’idar aiki, ya na mai cewa tuni an magance matsalolin da ya kai ga kama Isma’il Dikko.

Sai dai wani babban jami’i a helkwatar EFCC ya shaida wa manema labarai cewa, akwai akalla kararraki biyar a gaban hukumar a kan KASUPDA da shugaban ta.