Home Labaru An Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Matakin Shari’A Kan Badakalar Pandora

An Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Matakin Shari’A Kan Badakalar Pandora

11
0

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya CISLAC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakin shari’a a kan mutanen da binciken takardun badakala na Pandora ya bankado.

A makon da ya gabata ne aka fitar da bayanan, wanda gamayyar ‘yan jarida da masu rajin yaƙi da rashawa a duniya su ka bankado a kasashe sama da 90.

Kimanin mutane 300 ciki har da sama da mutane 100 ‘yan Nijeriya binciken ya kwarmata.

Shugaban ƙungiyar Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja.