Home Labaru Buhari Zai Ziyarci Kasar Masar Tare Da Gwamnoni 3

Buhari Zai Ziyarci Kasar Masar Tare Da Gwamnoni 3

500
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Masar domin halartar wani taro a kan tsaro da cigaban nahiyar Afrika.

Taron wanda zai gudana a ranar 11 ga watan Disamba, zai mada hankali ne a kan  alakar da ke tsakanin zaman lafiya da cigaba a nahiyar Afrika da kuma yadda za a samar da hanyoyin karfafa dokokin da za su tabbatar da tsaro tare da kawo cigaba ga kasashen Afrika.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya bullo da shirin a matsayin sa na shugaban kungiyar hadin kan kasashen Afrika.

Ana kuma sa ran shugabannin kasashen nahiyar Afrika da shugabanni daga kungiyoyi da hukumomin duniya da masana da kwararru daban-daban za su halarci taron domin tattauna a kan kalubalen da nahiyar Afrika ke fuskanta tare da samar da hanyoyin warware matsalolin.

Shugaba Buhari dai zai samu rakiyar gwamnan jihar Adamawa da takwaran sa na jihar Edo da na jihar Yobe.

 Sauran ragowar sun hada da Ministan tsaro Bashir Magashi da karamin ministan harkokin kasashen ketare Zubairu Dada, mai bawa shugaba kasa shawara a kan harkokin tsaro Babagana Monguno da kuma babban darektan hukumar leken aisri ta kasa NIA Ahmed Rufai Abubakar.

A karshe ana sa ran Buhari zai dawo Nijeriya a ranar Juma’a mai zuwa.