Home Labaru Kotu Ta Umurci Buhari Ya Bayyana Sunayen Min

Kotu Ta Umurci Buhari Ya Bayyana Sunayen Min

208
0

An bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari nada ministoci a kan lokaci kamar yadda doka ta tanada saboda gwamnatin sa ta biyu ta fara aiki gadan-gadan.

Wani lauya da ke Lagos, Kabir Akingbolu ne ya shigar da kara a kan Shugaba Buhari, inda ya bukaci kotu ta kaddamar da hukuncin cewa Buhari ya gaza nada adadin ministoin da doka ta tanada.

Karar da lauyan ya shigar dai ta hada da Atoni janar na tarayya, bayan ya yi watsi da jinkirin da aka samu wajen nadin ministocin.

Lauyan ya bukaci kotu ta umurci shugaba Buhari ya yi murabus idan bai shirya aiki daidai da kundin tsarin mulki ba, ya na mai cewa  shugaba Buhari  ya saba wa sashe na 147 da na 148 na kundin tsarin mulki na shekara ta 1999.

Lauyan ya kara da cewa, jinkirin ya kara haddasa mawuyacin halin da Nijeriya ke ciki, domin a cewar sa, lamarin ya janyo hukumomi da dama a kasar nan ba su samun kulawa.

Leave a Reply