Home Home Dokar Zaɓe: Majalisa Za Ta Ɗaukaka Ƙara A Kan Umarnin Kotu Na...

Dokar Zaɓe: Majalisa Za Ta Ɗaukaka Ƙara A Kan Umarnin Kotu Na Goge Sashe Na 84 (12)

626
0
Majalisar Wakilai ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na ba Ministan Shari’a Abubakar Malami umarnin goge sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta shekara ta 2022.

Majalisar Wakilai ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na ba Ministan Shari’a Abubakar Malami umarnin goge sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta shekara ta 2022.

Wata majiya ta ce, Majalisar ta kuma nemi ministan shari’a ya dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala ɗaukaka ƙara.

Kakakin Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya koka a kan dalilin da ya sa aka kai ƙarar kotun da ke Jihar Abiya, yana mai cewa majalisa ce kaɗai ke da ikon sauyawa ko yin doka a kundin tsarin mulkin Nijeriya.

A nata bangare, Majalisar Dattawa ta ce za ta ɗaukaka ƙarar bayan sanatoci da dama sun bijiro da buƙatar yin hakan a zaman su na ranar Larabar nan.

Majiyar ta ce, an an samu ‘yar hatsaniya a majalisar dattawa, lokacin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya buƙaci a cire sunan sa daga jerin waɗanda su ka amince a ɗaukaka ƙarar.

Leave a Reply