Home Labaru Dokar Fetur: Yankunan Da Ake Haƙo Fetur Ba Su Cancanci Kason Fiye...

Dokar Fetur: Yankunan Da Ake Haƙo Fetur Ba Su Cancanci Kason Fiye Da 3% Ba – Sylva

89
0
Timipre-Sylva1

Ƙaramin Ministan Man Fetur Timipre Sylva, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Dokar Inganta Fannin Man Fetur hannu ne don a gaggauta samun masu zuba jari.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja, Sylva ya ce a ranar Alhamis din nan, Shugaba Buhari zai yi bayani dalla-dalla a kan yadda dokar ta ke, da kuma duk abin da ya shige wa mutane duhu dangane da batun Rabon Arzikin Mai da ke ƙunshe a cikin dokar.

Da ya ke tsokaci dangane da al’ummar yankin Neja Delta, waɗanda su ka raina kashi 3 cikin 100 na rarar ribar fetur da ake haƙowa a yankin su, ministan ya ce bai ga abin tada jijiyar wuya a lamarin ba.

Ministan ya kara da cewa, daga yanzu fetur ne da kan sa zai riƙa yanka wa kan sa farashi a hannun ‘yan kasuwa.

Sai dai ya ce ba za a yi saurin fara amfani da sabuwar dokar ba tukunna, har sai an yi nazarin yadda za ta shafi talaka da kuma hanyoyin magance abin da zai iya biyo baya.