Home Labaru Martani: Babu Wanda Ya Ce Murtala Sule Garo Ne Zai Gaji Ganduje...

Martani: Babu Wanda Ya Ce Murtala Sule Garo Ne Zai Gaji Ganduje – Gwamnatin Kano

76
0
Garo-Ganduje

Gwamnatin jihar Kano, ta musanta rahotannin da ke cewa, uwargidan Ganduje Farfesa Hafsat Umar Ganduje ta ce Murtala Sule Garo ne zai maye gurbin mai gidan ta a karshen wa’adin mulkin shi.

Murtala Sule Garo dai shi ne kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukukomi da masarautu ta jihar ta Kano.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar, ya ce babu kamshim gaskiya a labarin da ake yadawa.

Ya ce Uwargidan Gwamnan ta yi farin ciki ne kawai da aikin Garo, da kuma goyon bayan sa ga manufofi da shirye-shiryen Gwamna Ganduje da gwamnatin sa a jihar Kano.

Sanarwar, ta ce an baddala abin da ke cikin bidiyon ta hanyar yin wani kirkirarren labari daga ciki, kuma mutane sun yi ta yada labarai da yawa musamman ta hanyar mutanen da ke son  haifar da rudani da tashin hankali domin haddasa rikici a jam’iyyar APC.

A karshe ya bukaci ‘ya jam’iyyar APC su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa, tare da karkatar da kuzarin su na tallafa wa gwamnatin wajen ci-gaba da yi masu hidima.