Home Labaru Takaddama: Gwamnatin Kaduna Na Shan Suka A Kan Shirya Taron Walimar Sanusi...

Takaddama: Gwamnatin Kaduna Na Shan Suka A Kan Shirya Taron Walimar Sanusi II

75
0
Photos-from-Sanusi-Lamido-Sanusis-60th-birthday-party

Ana ci gaba da cacar baki tsakanin ‘yan adawa da na gwamnatin jihar Kaduna, dangane da daukar dawainiyar walimar cika shekaru 60 ta tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.

Wasu ‘yan asalin jihar dai sun yi korafi a kan gudunmuwar da ake zargin gwamnatin jihar ta bada ta Naira miliyan 25 domin gudunar da taron walimar sarkin, wanda amini ne ga gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.

‘Yan jam’iyar ta PDP dai su na cewa, an yi facaka da makudan kudade wajen shagali, yayin da talakawa musamman ma’aikata ke cikin halin kuncin rayuwa.

Wani dan jam’iyyar PDP Mohammad Dan Auta, ya ce babu dalilin da zai sa gwamnati ta kashe wadannan kudade a kan shirya bikin taya abokin gwamna murnar zagayowar ranar haihuwar sa’.

Mai taimaka wa  gwamnan jihar Kaduna a kan harkokin siyasa a shiyya ta daya Mohammad Lawal Shehu, ya ce idan ma zargin ya tabbata ba laifi ba ne, duba da irin rawar da Sarki Sanusi ke takawa wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.