Home Labaru Dino Melaye Ya Maida Ma Wike Kakkausan Martini

Dino Melaye Ya Maida Ma Wike Kakkausan Martini

1
0

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Dono Melaye, ya maida
wa Gwamna Nysome Wike na jihar Rivers kakkausan
martani, dangane da furucin gwamnan na cewa Dino Melaye
ba ya da kimtsi da kamun-kai da natsuwar da zai iya zama
gwamna.

Yayin maida martanin, Dino Melaye ya ce Wike ya fi kowa sanin cewa ya cancanta, domin da ya fito takarar gwamna a shekara ta 2019 sai da ya ba shi gudunmawar Dala dubu 220, sannan ya sa aka ɗauke shi a jirgin shi daga Fatakwal har zuwa jihar Kogi a ranar zaɓen fidda-gwani

A wata hira da gidan talabijin na AIT, Sanata Melaye ya ce Wike ya na jin haushin sa ne saboda ya ƙi goyon bayan kudirin sa a takarar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a PDP.

Dino Melaye ya ce ya kamata mutane su tuna cewa shi ba sabon yanka ɗan siyasa ba ne, domin ya yi dan majalisar wakilai kuma ya yi Sanata sau biyu sannan ya yi hadimin shugaban ƙasa.

A ƙarshe ya shawarci Wike da cewa, a duk lokacin da ya yi mankas ya kiyayi yin Magana, saboda baki ya san abin da zai faɗa, amma bai san abin da za a maid ma shi ba.