Home Labaru Za a Sa Kyamarorin Tsaro Na n495m a Tashoshin Jirgin Kasan Abuja-Kano

Za a Sa Kyamarorin Tsaro Na n495m a Tashoshin Jirgin Kasan Abuja-Kano

1
0

Gwamnatin Tarayya ta amince a sanya na’urorin daukar hoton
kwakwaf na jikin fasinjoji da kayayyakin su a tashoshin jirgin
kasa da ke jihohin Kano da Kaduna.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin kashe Naira miliyan 495, wajen sayowa da sanya na’urorin a tashoshin jirgin kasa da ke jihohin Kano da Kaduna da kuma Abuja.

Minista a Ma’aikatar Sufuri Ademola Adegoroye, ya ce Majalisar Zartarwa ta Kasa ta bada izinin fitar da kudin domin sayo na’urorin tsaron ne, da nufin tabbatar da aminci ga matafiya duba da yanayin tsaro da ake fama da shi a yankin.

Ya ce na’urorin sun hada da wadanda fasinjoji za su bi ta ciki a ga hoton kwakwaf na abin da su ke dauke da shi a jikin su, da wadanda za su dauki hoton kwakwaf na jakunkuna da sauran kayan matafiya, sai kuma wadanda jami’an tsaro za su rike a hannu domin caje matafiya.

Ademola Adegoroye, ya ce za a yi hakan ne domin hana yiwuwar wani ya shiga jirgin ya yi wa matafiya barna.