Home Labaru Neman Mafita: Zulum Ya Nuna Damuwa A Kan Hare-Haren ‘Yan Boko Haram

Neman Mafita: Zulum Ya Nuna Damuwa A Kan Hare-Haren ‘Yan Boko Haram

236
0
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwa game da hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kai wa akananan hukumomi cikin ‘yan kwanakin nan.

Babagana Zulum ya bayyana damuwar sa ne, yayin da gamayyar kwamitocin tsaro na majalisun dokoki na tarayya a karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume su ka ziyarci jihar Borno.

Ya ce jami’an sojin Nijeriya su na kokari, sai dai akwai bukatar a kara kaimi domin tabbatar da ganin an kawo karshen hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kai wa jama’a.

Gwamnan ya cigaba da cewa, sun samu kwararan bayanan da ke cewa, ‘yan Boko Haram sun yi yunkurin kai wani hari a garin Gubio, wanda jami’an soja su ka dakile, ya na mai cewa dole ne a samar da mafita a kan wannan lamari.