Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce za ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi a ranar 2 Ga Nuwamba na shekara ta 2019.
Kakakin Yada Labarai na hukumar zabe ta kasa Festus Okoye ne ya bayyana haka a Abuja.
Ya ce bayan Shugabannin INEC sun gudanar da taro, hukumar ta fito da jadawalin yadda zabubbukan za su kasance, tun daga zaben fidda-gwani har zuwa na gama-gari.
Hukumar zaben ta ce za ta fitar da sanarwar fara hada-hadar zaben a ranar 1 ga watan Agusta, kuma duk jam’iyyar da ke sha’awar shiga takara za ta yi zaben fidda-gwani tsakanin ranar 2 zuwa 29 ga watan Agusta.
Haka kuma, hukumar ta ce ta na bukatar duk jam’iyyar da za ta shiga zaben ta aika da sunayen wakilan ta zuwa ranar 2 ga Oktoba.
INEC ta ce a cikin watan Mayu za ta yi gagarimin aikin nazari da kuma bin diddigin yadda zaben 2019 ya gudana.
You must log in to post a comment.