Kungiyar masu hakar ma’adinai ta Nijeriya, ta ce za ta ba gwamnatin tarayya hadin kai, dangane da umurnin da ta bada na tsaida ayyukan hake-haken ma’adanai a jihar Zamfara.
Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Kabir Kankara ya bayyana haka a Abuja.
Gwamnatin Tarayya dai ta bada umurnin dakatar da ayyukan hake-haken ma’adanai a jihar Zamfara ne ranar 7 ga watan Afrilu.
Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammed Adamu, ya ce umurnin ya na daga cikin matakan da aka dauka na magance lamarin ta’addanci a jihar Zamfara.
Alhaji Kabir Kankara, ya ba gwamnati da hukumomin ta tabbacin cewa, a shirye kungiyar ta ke ta ba su hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwazo a fannin hakar ma’adanai.
You must log in to post a comment.