Home Labaru Zamfara: Rundunar Sojin Sama Ta Fara Atisayen ‘Operation Tsaftar Daji’

Zamfara: Rundunar Sojin Sama Ta Fara Atisayen ‘Operation Tsaftar Daji’

329
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta ce ta fara atisayen ‘Operation Tsaftar Daji’ domin fatattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso Yammacin Nijeriya, kamar yadda jami’in rundunar Napoleon Bali ya bayyana.

Ya ce kowa ya san yadda gwamnati ta maida hankali wajen kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a dazuzzukan yankin Arewa Maso Yamma, amma miyagun mutanen su na neman su maido wa gwamnati hannun agogo baya.

Jami’in ya kara da cewa, za su yi amfani da jiragen sama domin fatattakar irin wadancan miyagun mutane da ruguza maboyar su a dazuzzukan.

Ya kuma yi kira ga mutane su cigaba da sama wa rundunar bayanai masu amfani domin samun nasara a aikin da su ka sa gaba.

Ya ce sun tanadi manyan jirage masu amon wuta ta ko-ina da kuma wasu zaratan makamai don ganin sun ragargaza ‘yan ta’addan da ke addabar al’umma.