Home Labaru An Yi Jayayya Tsakanin Bangaren Buhari Da Atiku A Kotu

An Yi Jayayya Tsakanin Bangaren Buhari Da Atiku A Kotu

567
0

A zaman sauraren shari’ar zaben shugaban kasa na shekara ta 2019, an samu jayayya tsakanin bangaren shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar game da wani bidiyo da Atiku ya nemi ya nuna a kotu.

Rahoton sun ce lauyan jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar Chris Uche ya nemi kotu ta ba shi damar nuna wasu bidiyo da ke nuna yadda jam’iyyar APC ta tafka magudi a rumfunan zabe.

Haka kuma, lauyan ya nemi kotun ta amince da tsohon kakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar Segun Sowunmi a matsayin babbar shaida na farko.

Karanta Labaru Masa Alaka: Atiku Ya Lallasa Shugaba Buhari A Jihar Katsina – Majigiri

Sai dai fadin haka keda wuya, lauyan APC Adeniyi Akintola, da lauyan hukumar zabe Ustaz Yunus da lauyan shugaba Buhari Alex Izinyon, sun yi wa lauyan PDP caa, tare da bukatar kotu ta yi watsi da bukatar sa.

Idan dai za a iya tunawa, tun a makon da ya gabata ne Atiku ya nemi kotu ta ba shi damar nuna wasu bidiyo da zai fallasa yadda jam’iyyar APC da shugaba su ka shirya magudi a wasu rumfunan zabe, wanda ya ce hakan ne ya haifar da aringizon kuri’u da su ka ba su nasara a zaben shekara ta 2019.