Home Labaru Difilomasiyya: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi A Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Difilomasiyya: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi A Zauren Majalisar Dinkin Duniya

19
0


Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai yi jawabi a wajen taron majalisar dinkin Duniya karo na 76 da zai gudana a helkwatar ta da ke birnin New York na kasar Amurka.

Buhari dai ya na daga cikin wadanda aka zaba su gabatar da jawabi a zauren taron a ranar 24 ga watan Satumba na shekara ta 2021.

Wata majiya ta ce, shugaba Buhari ne mutum na biyu da zai yi jawabi a rana ta hudu na taron, wanda zai gudana a kasar Amurka.

Majiyar ta kara da cewa, ana sa ran shuga ba Buhari zai yi jawabi ne da misalign karfe biyu na rana agogon Nijeriya.