Home Labaru Tsaro: Buhari Na So A Yi Doka Kan Shigar Da Makamai Da...

Tsaro: Buhari Na So A Yi Doka Kan Shigar Da Makamai Da Ababen Fashewa Najeriya

14
0

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawan bukatar gwamnati ta yin doka da za ta sa ido kan shigo da kananan makamai, da kuma saye da sayar da abubuwan fashewa.

Kudurorin biyu sun hada da ‘sa ido kan kananan makamai da kuma ‘ababen fashewa’.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmed Lawan ne ya karanto wasikar da ke kunshe da kudurorin a zaman majalisar bayan dawowarsu daga hutun wata biyu.

A cikin wasikar, Shugaba Buhari ya ce ”akwai bukatar sa ido kan yadda ake samarwa da ajiyewa da mallaka da amfani da rabawa da saye da kuma sayar da ababen fashewa.”

Bugu da kari wasikar ta bukaci a mayar da kwamitin Shugaban Kasa kan Kananan Makamai zuwa Cibiyar Lura da Kananan Makamai ta Kasa, da za ta yi aiki a karkashin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsa