Home Labaru Difilomasiyya: Sanata Ahmed Lawan Ya Gana Da Jakadan Kasar China A Nijeriya

Difilomasiyya: Sanata Ahmed Lawan Ya Gana Da Jakadan Kasar China A Nijeriya

652
0
(L) Jakadan Kasar China A Nijeriya Zhou Pingjian (R) Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Lawan Ahmad

Shugaban majalisar dattawa Sanata Lawan Ahmad, ya ce harkar kasuwanci da ke tsakanin kasashen Nijeriya da China ta na bukatar daidaituwa.

Da ya ke bayani yayin karbar bakuncin jakadan kasar China a Nijeriya Zhou Pingjian, Sanatan ya ce daidaita lamurran kasuwanci tsakanin kasashen biyu ne kawai zai bada damar samun cinma abubuwan da ake bukata.

Shugaban majalisar, ya kuma kara da rokon gwamnatin kasar China ta mara wa kokarin da Shugaba Buhari ke yi baya domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce duk da cewa kasashen biyu sun kasance su na alaka da juna na tsawon lokaci, amma abin damuwa ne ta yadda a bangaren kasuwanci alakar ta samu tawaya a yanzu.

Da ya ke na shi jawabin, Jakada Pingjian ya jinjina wa Nijeriya a kan tsarin da ta kaddamar na ‘One China policy’, inda ya ce tsari ne mai kyau da zai inganta alaka tsakanin Nijeriya da China.

Leave a Reply