Home Labaru Kiwon Lafiya Kanjamau: Za A Rika Karbar Magani Kyauta A Jihar Rivers – Wike

Kanjamau: Za A Rika Karbar Magani Kyauta A Jihar Rivers – Wike

449
0

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce daga yanzu duk masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki HIV, za su rika karbar magani kyauta a jihar.

Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers

Wike ya bayyana haka ne, a lokacin da tawagar hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka ta ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar da ke Fatakwal.

Ya ce Kasar Amurka za ta tallafa masu da magungunan cutar kyauta, wanda hakan ya sa za su daina karbar kudade daga hannun masu fama da cutar.

Idan dai ba a manta ba, sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, jihar Rivers na cikin jihohin da su ka fi fama da wadanda su ka kamu da wannan cuta.

Sakamakon binciken, ya ce jihar Akwa-Ibom ce ta fi kowace jiha yawan mutanen da ke dauke da cutar, sai kuma jihar Benue da ke biye da ita.

Jagoran tawaga Tedd Elerbrock, ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa, adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar a jihar Rivers ya kai dubu 210, kuma daga cikin su mutane 40,000 ne kawai ke samun magani kai tsaye.

Leave a Reply