Home Labaru Makamai: Gwamnoni Sun Yi Wa Amosun Raddi Game Da Tara Makamai

Makamai: Gwamnoni Sun Yi Wa Amosun Raddi Game Da Tara Makamai

909
0

Gwamnonin Nijeriya sun maida wa tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun aniyar sa, bayan ya yi furucin cewa gwamnoni na gina manyan rumbunan ajiyar makamai a Gidan Gwamnati.

Amosun ya yi zargin ne, a lokacin da ya ke kokarin wanke kan sa daga zargin boye tulin makamai a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.

Makaman, wadanda ya sayo da kudin gwamnati a asirce ya kuma kimshe ba tare da sanin jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro ba babban laifi ne, kuma karya dokar safarar makamai ce karara.

Manyan jami’an tsaron Nijeriya dai sun cika da mamakin yadda Amosun ya shigo da makaman ta haramtacciyar hanya, da kuma tababar abin da aka yi niyyar yi da su. Gwamnatocin jihohin Ondo da Osun da Lagos da Oyo da Ekiti da Ogun dai sun karyata Amosun, inda su ka ce ba su taba sayo makamai a asirce su ka boye a asirce kamar yadda Amosun ya ce ana yi ba, domin hakan ba ya cikin ayyukan da doka ta dora wa gwamnoni.