Home Labaru Difilomasiyya: Goodluck Jonathan Ya Isa Mali Domin Sasanta Rikicin Siyasa

Difilomasiyya: Goodluck Jonathan Ya Isa Mali Domin Sasanta Rikicin Siyasa

152
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya isa birnin Bamako na ƙasar Mali, domin shiga tsakani a rikicin siyasar da ke ci-gaba da ta’azzara a ƙasar.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Ana sa ran Jonathan zai tattauna da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da shugabannin jam’iyyun hamayya da ƙungiyoyin fararen hula da kuma malaman addini.

Kasar Mali dai ta faɗa cikin rikicin siyasa a makonnin baya-bayan nan, inda masu zanga-zanga ke kira ga Shugaba Keïta ya sauka daga mulki bisa batutuwa da dama ciki har da zaben da ake ce-ce-ku-ce a kan sa.

Masu zanga-zangar, sun samu kwarin gwiwa ne musamman saboda gazawar gwamnati wajen shawo kan rikicin kabilanci da na addini da ke addabar kasar.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas, Jean-Claude Kassi Brou ya sanar da Wakilicin Goodluc Jonathan.