Home Labaru Ambaliya: Jihohin Adamawa Da Taraba Sun Fuskanci Ambaliyar Ruwa

Ambaliya: Jihohin Adamawa Da Taraba Sun Fuskanci Ambaliyar Ruwa

450
0

Al’ummar wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba dake arewa maso gabashin kasar nan sun fara kokawa tare da yin kira ga gwamnati da a kai musu dauki sakamakon ambaliyar ruwan da suka fara fuskanta.

A baya dai hukumar kula da yanayi ta kasa da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, sun yi gargadin cewa akwai yuwuwar samu mummunan ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar nan.

Wasu mazauna garin Yola, babban birnin jihar Adamawa da kuma karamar hukumar Lau a Jihar Taraba sun fara fuskantar ambaliyar.

A zantawar su da manema labarai wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa sun ce ambaliyar ruwan ta samo asali ne sakamakon toshe magudanan ruwa da Al’umma ke yi.