Tsohuwar ministar man fetur diezani alison-madueke, ta kama hanyar maido da kadarorin ta da gwamnatin tarayya ta ƙwace.
Diezani ta yi hakan ne ta hanyar shigar da ƙara, inda ta buƙaci wata babbar kotun tarayya ta janye umarnin da ta ba hukumar efcc na ƙwace mata kadarori.
Tsohuwar ministar ta shigar da buƙatar neman kotun ta dakatar da hukumar efcc daga saida kadarorin da ta ƙwace mata, ta na mai cewa an yaudari kotunan ne wajen bada umarnin kwace kadarorin ta, ta hanyar danniya ko kuma rashin bayyana gaskiyar lamarin ga duniya.
Wata majiya ta ce, efcc ta na shirin saida kadarorin diezani da ta ƙwace ga mabuƙata, daga ranar 9 ga janairu kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin sanarwar da hukumar ta fitar.
A nata ɓangaren, hukumar efcc ta nemi kotu ta yi watsi da ƙarar da tsohuwar ministar ta shigar.