Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa Idris Isah Jere, ya sake gargadin masu tatsar mutane kudi a ofisoshin fasfo, ya na mai jaddada cewa duk wanda aka kama zai dandana kudar sa ko yanzu ko nan gaba.
Idris Jere ya bayyana haka ne a Legas, yayin kaddamar da ofishin tattara bayanan fasfo tare da shigar da su a manyan cibiyoyin wallafa fasfo a Alimosho da ke Legas.
Ya ce Ofishin fasfo ba wuri ne da marasa gaskiya za su iya rabuwa ba, haka nan masu ci da gumin wasu ko ‘yan ba-ni-na-iya ko kuma duk wani mutum da ba a aminta da sahihancin sa ba.
Ya ce doka ba za ta sarara wa duk wanda aka kama da hannu wajen aikata laifuffuka ko saba ka’idodjin fasfo ba, kamar yadda ya ke kunshe a cikin dokar shige da fice sashe na 10, karamin sashe na 1.
Idris Jer ya yi alkawarin cewa, hukumar za ta cigaba da gudanar da nagartattun ayyuka ga ‘yan Nijeriyan da su ke mu’amala da su.
You must log in to post a comment.